Potato lollipop (dankali me samfurin lollipop)

Source : A Feraye Bayan Dankalin Ayi Masa Yankan Gida Huda A Zubashi A Cikin Ruwa Sannan A Wanka A Zuba A Tukunya A Zuba Ruwa A Dafashi Har Sai Ya Dahuwa Amma B...

PreTime
more Minutes
CookTime
a few Minutes
Yield
Some Servings

Sent by

at : April 11, 2026

Step:

  1. A feraye bayan dankalin ayi masa yankan gida huda a zubashi a cikin ruwa. Sannan a wanka a zuba a tukunya a zuba ruwa a dafashi har sai ya dahuwa amma ba luguf ba sai a tsane a kwalanda.

  2. A dauko nikakken nama a wanke sannan dafashi da kayan kamshi, magi da albasa Idan ya dahuwa shima a ajiye guru daya Idan da ruwa a ciki a tsaneshi daga cikin ruwan.

  3. A juye dankalin a roba me tsafta sai a marmasashi sannan a zuba naman a ciki, a kawo jajjagen a zuba, a saka kayan kamshi da kori kadan amma, sai a juya, Idan magi bejiba ba sai a kara a juya ya hade jikinsa.

    Potato lollipop (dankali me samfurin lollipop)matakin girki3 hoto
  4. A dunga mulmula hadin ana amaidashi kamar kwallo a ajiye a gefe, Idan yana kama Hannu sai a dunga dangwalar mai a hannun.

    Potato lollipop (dankali me samfurin lollipop)matakin girki4 hoto
  5. A Dora mai akan wuta a saka albasa, a sami kwano a fasa kwai a saka spices a yayyanka albasa kanana sai a kadashi sama sama..

  6. Idan ya yi zafi sai a dauko dunkulen dankalin a saka shi a ruwan kwai sannan a barbadeshi da Garin burodi sannan a sake sakawa a ruwan kwai sai a saka a mai a soya. Idan ya koma ruwan Zuma sai a kwashe. A rage wutar sabida cikin ya soyu.

  7. Idan aka kwashe man ya tsane sai a dauko tsinken tsire ko na sakace a soka a tsakiyar dankalin.

    Potato lollipop (dankali me samfurin lollipop)matakin girki7 hoto

Ingredients

  1. 8 Dankalin turawa manya guda
  2. 1/2 cup Nikakken nama
  3. Kayan dandano
  4. Kayan kamshi
  5. Kori
  6. Jajjagaggen attaruhu da albasa cokali 1
  7. Mai domin suya
  8. Tsinken yin tsire ko na sakace
  9. Kwai guda 2 manya
  10. Garin burodi (bread crumb)

Related Recipes

Nannadadden doughnut

Nannadadden doughnut

Paw-paw fruits salad bowl

Paw-paw fruits salad bowl

Macaroni salad

Macaroni salad

Lemon goba na musamman me whipping cream

Lemon goba na musamman me whipping cream

Balangun zamani me juicyromo romo

Balangun zamani me juicyromo romo

Taliya da macaroni me alayyahu da dambun nama

Taliya da macaroni me alayyahu da dambun nama

Cabbage and onion noodles

Cabbage and onion noodles

French toast + yam ball

French toast + yam ball