Source : Tuwo Ki Wanke Shinkafarki Ki Gyarata Ki Daura Ruwanki In Tafasa Ki Zuba Shikafarki In Tadahu Sosai Ki Tukata Ki Kwashe Kisa Aledamiya Da Farko Zaki Sur...
PreTime
more Minutes
CookTime
a few Minutes
Yield
Some Servings
Sent by hafsat tahir salga
at : November 20, 2025
Step:
Tuwo. ki wanke shinkafarki ki gyarata ki daura ruwanki in tafasa ki zuba shikafarki in tadahu sosai ki tukata ki kwashe kisa aleda
Miya da farko zaki surfa waken ki k wanke shi tas ki daura a wuta ya dahu sosai
Sai ki blending kayan miyarki ki daura kisa mai dasu Maggie da spices kisa ruwan namanki ki kawo daddawa kisa yar kadan ki barshi ya dahu kisa gyadanki ta miya bayan kin daka ta itama kadan saboda ba miyar gyada bace ina sa gyada da daddawa a miyar wake ne Dan yana bada wani sina dari mai dadi
Saiki kawo wakenki Wanda dama ya riga ya dahu kisa kisa curry dinki da tyme sai ki kawo zogale shima ba dayawa ba ki zuba sai ki rufe in tayi ki sauke.