Source : Da Farko Zaki Yi Parboiling Rice Dinki Ki Tace Ta Ki Aje A Gefesai Ki Sami Tukunya Ki Zuba Mai Aciki Kisa Tafarnuwa Da Kika Grating Dinta In Tafara Soyu...
PreTime
more Minutes
CookTime
a few Minutes
Yield
Some Servings
Sent by hafsat tahir salga
at : November 19, 2025
Step:
Da farko zaki yi parboiling rice dinki ki tace ta ki aje a gefe
Sai ki sami tukunya ki zuba mai aciki kisa tafarnuwa da kika grating dinta in tafara soyuwa kisa albasa
In albasar ta danyi laushi sai ki zuba kayan miyarki wanda kika yi grating dinsu dama na raba su biyu nayi grating rabi na yanka rabi to sai ki fara zuba na grating din ki soya su
Inya soyu sai ki dauko Wanda kika yanka ki zuba yankakkun kayan miya suna bada wani kanshi na daban a jollof to saiki soya su.
In suka yi saiki zuba seasoning dinki
Sai ki dauko ruwan naman ki ki zuba ki tsaida ruwan yadda zai dafa miki shinkafarki gashi na zuba gram masala spices dina
Sai na zuba curry wannan hadin gida ne akwai kamshi
Sai na zuba nama na Wanda na soya shi sama sama
Bayan ruwan ya tafasa na kawo shinkafata wadda dama na riga da na mata rabin dahuwa sai na zuba na rufe yanka na zuba
Na zuba tyme,na kara curry
Na zuba vegetables dina Wanda dama na ruga na tafasasu da baking powder saboda kalar su ta fito.na yanka green paper na na zuba nasa albsa wadda itama na yanka na rufe
To gashi jollof rice dinmu tayi sai na sauke zaki ji tana bada wani kamshi na musamman
Gashi sai nasa hadin salad dina a gefe Ku gwada akwai dadi sosai