Source : Ga Kayayyakin Da Muke Bukata Na Hadasu Guri 1 Ba Sai Na Fara Ma Dunga Kicin Kicin Daukowa Baza A Fara Da Gyara Naman Tsattsaga Shi Kamar Yanda Nayi A K...
PreTime
more Minutes
CookTime
a few Minutes
Yield
Some Servings
Sent by Khady Dharuna
at : August 11, 2026
Step:
Ga kayayyakin da muke bukata na hadasu guri 1. Ba sai na Fara ma dunga kicin kicin daukowa ba
Za a Fara da gyara Naman tsattsaga shi kamar yanda nayi a kasa a hoto
Sannan a kawo hadin yajin nama, daddawa, citta a juya
Sai a zuba akan naman
Sannan a zuba kanumfari, masoro, cardamom, da bay leef
A zuba everything mix spices
A saka suaran ma da sukai ragowa
A marmasa Maggie a kai
Sannan a kawo gudar tafarnuwa da aka bare a zuba a kai
A zuba gogaggiyar albasa
Sannan a kawo bama cokali 1 a zuba akai
Sai a zuba ruwan lemon tsami a juya, ko Ina ya hade. A rufe a barshi ya tsumu. Idan so samune ya kwana ki yayi awa 12 Haka.
A dauko abin gashi a shimfida foil paper. Dalilin shimfidawar sbd kar romon ya fita. Sai a zuba Naman a Kai a yayyanka albasa ba a saka Mai d akansa Zai fitar da Mai, sai a gasa a wuta kadan a hankali a hankali Zia gasu
Idan ya gasu za a ga yayi juicy sosai. Baya bukatar a Kara yaji. Saidia za a iya ci a yayyanka tumatir da cucumber.
Nidai a lokacin inaci Ina hadawa da pizza, recipe din pizza Yana hanya in Sha Allah.