Source : Zaki Jika Wakenki Ki Surfa Ki Wankesai Ki Juye A Blender Ki Sakata Tarugu Da Albasa Da Tafarnuwa Idan Kina Bukata Ki Markadaidan Yayi Laushi Sosai Sia K...
PreTime
more Minutes
CookTime
a few Minutes
Yield
Some Servings
Sent by Khady Dharuna
at : June 8, 2026
Step:
Zaki jika wakenki ki surfa ki wanke
Sai ki juye a blender ki sakata tarugu da albasa da tafarnuwa idan kina bukata ki markada
Idan yayi laushi sosai Sia ki juye a roba ko kwano
Sannan ki kawo soyayyen manja ki zuba a kai
Sannan ki zuba soyayyen man gyda
Sai ki saka kayan dandano
Sannan kayan kamshi
Kamar spices, seasoning, curry, fennel seed
Ki juya ya hade guri 1
Ki fasa kwai ki sa magi da spices da albasa ki kada
Sai ki dauko abin da za ki turara ki shafa Masa mai
Sannan ki zuba hadin kullum a ciki ki kawo ruwan kwannan ki zuba akai
Sannan ki kawo ragowar kayan hadin dama kin wanke kin yayyanka ki zuzzuba akai
Sai ki samu babbar tukunya ki zuba ruwa Dan daidai ki Dora murfin tukunya ko dan Abu me tudu kadan. Snanan ki Dora hadin alalar ki rufe
Ki sa wuta kadan a hankali Zai gasu
Zkai iya ci Haka za Kuma ki iya ci da manja da yaji