Source : Ga Kayayyakin Da Muke Bukata Nan Za A Fara Da Feraye Dankali A Wanke A Gudansa In So Samu Ne A Zabo Madaidiata Sia A Sami Abin Kwakule Dnakali A Kwaku...
PreTime
more Minutes
CookTime
a few Minutes
Yield
Some Servings
Sent by Khady Dharuna
at : May 15, 2026
Step:
Ga kayayyakin da muke bukata Nan.
Za a fara da feraye dankali a wanke a gudansa. In so samu ne a zabo madaidiata. Sia a Sami abin kwakule dnakali a kwakule tskaiyar.
Sai a Dora ruwa a zuba a dafa shi sama sama kae yayi luguf dai, Amma a kula kar a cika wuta sbd Nan da Nan yake dahuwa, idan ya tahu sai a tace a kwalanda
A Dora tukunya me tsafta a zuba Mai a ciki
Sannan a zuba fennel seed a juya
Sai a zuba albasa a motsa na Yan mintuna
Sannna a goga Kara's Bayan an kankare Bayan an wnake, a zuba a motsa
Sai a kawo marmasasshen kifi shima a zuba akai
A zuba kayan dandano da kayan kamshi a cigaba da soyawa har ya Zama ya soyu sai a juye a kwano
Bayan ya Sha iska sai a dauko dankalin a dunga cusa hadin a cikin Ramin a hankali sbd kar ya fashe. Ayi ta Yi har a gama
Sai a kada kwai a zuba Maggie da spices, a yanka albasa a saka ragowar Kara's dinnan.
Sai a tsoma dankalin a ciki a jujjuya koina ya ji
Sannnan a saka a cikin garin bread a jujjuya koina ya rufe
Sai a sake sakawa a ruwan kwai a sa a Mai me zafi a soya. Idna yayi alamar soyuwa sai a kwashe.
Masha Allah
Dadi sai ma kin gwada zaki banbance dadin sa da normal dankali