Source : Dafarko Zakisa Fulawa A Roba Kisa Mai Da Gishiri Da Yis Kadan Saiki Murzasu A Hannunki Su Hade Saiki Rika Zuba Zuwa Kina Kwabawa Harsai Yayi Laushi S...
PreTime
more Minutes
CookTime
a few Minutes
Yield
Some Servings
Sent by Umman Amir And Minaal
at : February 26, 2026
Step:
Dafarko zakisa fulawa a roba, kisa mai da gishiri da yis kadan, saiki murzasu a hannunki su hade.
Saiki rika zuba zuwa kina kwabawa harsai yayi laushi saiki aje kamar na minti talatin, gashinan ya tashi.
Saiki raba gida 6 ko 7, ki murza yayi fadi, kidora pan a wuta saiki dora Wanda kk murza akai
In ya fara gasuwa zakiga ya fara haka, saiki juya dayan gefen inya gasu ki cire a wuta kisa a Leda kisa a kula saboda karya bushe, haka zakiyi saikin gama gasawa
Ki yanka nama kanana kisa mai kadan kisa naman kisa maggi 1 da curry kadan, kisa albasa da tarugu kiyita juyawa saiya yi kamar kin soya saiki sauke, ki fara kwai ki soya amma ki dagargazashi,ki kwashe, ki yanka cabbage da carrot da koren tattasai., ga kayanmu
Kisa mayyonise a bowl, kisa ketchup, da black pepper, saikiyi juya su hade sosai
Ki kawo shawarma bread dinki ki shafa wannan hadi na mayyonise, saikisa cabeji, kisa karas
Kisa koren tattasai, kisa hadin kwai, kisa nama,saiki nade, ki rufe rabin da tissue
Aci dadi lafiya
Nayi amfani da mayyonise hadin gidgida, yadda zaki hada, kwai 1, farin ruwan kal kadan, mangyada, lemon tsami rabi, gishiri da sugar kadan, ki fasa kwai a bilenda kisa gishiri da sugar da kal da lemon tsami saiki nika kamar na minti 3 zakiga yayi fari, saiki rika sa mangyada kina nikawa harsai yayi kaurin da kikeso saiki kashe ki juye a roba