Source : Zaki Tankade Filawar Ki Kisa Bakar Huda Gishiri Sikari Da Mai Ki Motsa Sosai Sai Kisa Ruwa Amma Da Kadan Kadan Zakina Zubawa Kina Motasawa Har Ya Dade J...
PreTime
more Minutes
CookTime
a few Minutes
Yield
Some Servings
Sent by Sumy's delicious
at : October 12, 2026
Step:
Zaki tankade filawar ki kisa bakar huda,gishiri,sikari da mai,Ki motsa sosai Sai kisa ruwa amma da kadan kadan zakina zubawa kina motasawa har ya Dade jikan sa Dan kar ki cika Sai ki rufe shi na mintuna 10 kafin ki fara murzawa
Sai ki mu gutsirasu kana na kamar haka Sai ki murza sosai,ki kula: kar kirkiyi shi da kauri filan sosai akeson amurza shi Sai ki yanka daga sama amma karya kai karshe Sai ki barbada filawa
Ki matse karshen bakin kamar haka Sai ki kitsa shi har karshe Sai ki hade baikin biyu shknan Sai ki soya a mai me zafi
Ki daura ruwa a tukunya kisa lemon tsami ko tsamiya da sikari yayi ta dahuwa har Sai kinga yafara kunfa yayi kuma kauri Sai ki tsoma Diblan dinki aciki shikenan kingama, Idan lemon tsami kikayi amfani dashi zaki iya sa kala aciki shknn Sai ci