Bredin kabewa meh rose

Source : Da Farko Ki Wanke Kabewan Ki Seh Ki Zuba A Steamer Ki Turarashi Har Seh Ya Dahu Seh Ki Farfasa Shi Da Chokali Meh Yatsu Ya Farfashe Ki Aje Gefe Seh Ki ...

PreTime
more Minutes
CookTime
a few Minutes
Yield
Some Servings

Sent by

at : August 4, 2026

Step:

  1. Da farko ki wanke kabewan ki seh ki zuba a steamer ki turarashi har seh ya dahu,seh ki farfasa shi da chokali meh yatsu ya farfashe ki aje gefe.

    Bredin kabewa meh rosematakin girki1 hoto Bredin kabewa meh rosematakin girki1 hoto
  2. Seh ki samu kofi ki hada hadin. Yeast dinki a ciki ki zuba ruwan da yeast da sikari ki juya kibarshi tsawon minti 5 har seh ya kumburo.seh ki samu roba meh fadi ki tankade flour a ciki ki zuba sikari da baking powder seh ki zuba hadin yeast da butter da kabewan a ciki.

    Bredin kabewa meh rosematakin girki2 hoto Bredin kabewa meh rosematakin girki2 hoto
  3. Seh ki zuba sauran ruwan a ciki ki kwaba har seh ya hade jikinsa.ki shafa mai kadan cikin roban seh ki maida kwabin flour din ciki ki rufe da kling film ya tashi tsawon minti 45.

    Bredin kabewa meh rosematakin girki3 hoto Bredin kabewa meh rosematakin girki3 hoto
  4. Idan ya tashi seh ki kara kneading kwabin tsawon minti 3 ko 4,ki raba shi gida uku seh ki mulmula kowanne ki aje.seh ki dauki daya ki murzashi yayi tsawo seh ki raba gida biyar.Haka za kiyi da sauran.

    Bredin kabewa meh rosematakin girki4 hoto Bredin kabewa meh rosematakin girki4 hoto Bredin kabewa meh rosematakin girki4 hoto
  5. Seh ki dauki kowane hadin flour da kika raba gida biyar ki fadadashi ki aje gefe har seh kin fadada guda biyar.seh ki dakko daya ki aje ki sake dako wani ki daura akai haka zakiyi har ki jera guda biyar din kina dan danna shi kadan in kin daura kan daya.seh ki nadeshi a hankali kamar tabarma kina danna bakin ya hade har ki nade shi gaba daya seh ki dan murza shi bakin ya hade.

    Bredin kabewa meh rosematakin girki5 hoto Bredin kabewa meh rosematakin girki5 hoto
  6. Seh ki sa wuka ki yanka shi gida biyu daga tsakiya zeh baki siffar rose seh ki gyagyara yanda zeh baki ganyan rose din kina dan bubudesu da hannun ki.

    Bredin kabewa meh rosematakin girki6 hoto
  7. Seh ki samu parchment paper ki yankasu ki daura kowane rose akan guda daya.seh ki jera su cikin saman steamer ki samu kitchen cloth ki rufe saman ki barshi ya kara tashi na minti 30

    Bredin kabewa meh rosematakin girki7 hoto Bredin kabewa meh rosematakin girki7 hoto
  8. Bayan minti talatin seh ki cire kitchen cloth din ki rufe da murfin steamer din.seh ki zuba ruwa cikin kasan steamer din ki daura tukunyar saman meh bredin rose din.ki turarashi a high heat na minti 20 zuwa 25.seh ki kashe wutar ki dan bude murfin yadda turirin zeh rika fita tsawon minti 2 ko 3.saboda kar suyi shrinking.seh ki sauke,a ci lafiya.

    Bredin kabewa meh rosematakin girki8 hoto

Ingredients

  1. 70 g Kabewa bararre
  2. Hadin yeast:
  3. 3 g Yeast
  4. 5 g Sikari
  5. 45 g Ruwan dumi
  6. Hadin flour:
  7. 190 g Flour
  8. 30 g Sikari
  9. Baking powder 1/2 karamin chokali
  10. 15 g Bota

Related Recipes

Tsala

Tsala

Shepherds pie

Shepherds pie

Dublan

Dublan

Chicken pepper soup

Chicken pepper soup

Home made lemon oil

Home made lemon oil

Healthy sugar free Granola

Healthy sugar free Granola

Shredded beef sauce da couscous

Shredded beef sauce da couscous

Parpesun naman akwiya

Parpesun naman akwiya