Da farko ki wanke kazarki ta tsane tas seh ki hada jajjagenki yadda kike bukata da mayyonaise,dandano,spices,soysauce.Seh ki shafe kazarki ko ina ya ji bayan kin tsaga wurin tsokar dan hadin ya ratsata.kafin nan ki dibi hadin kadan ki aje saboda shafawa a jikin kazar yayin gashi kuma ki dan hada cikin dankalin.seh ki samu leda ki sata ki rufe ki sa a roba ki sa a fridge ta kwana.