Source : Da Farko Ki Hada Kayan Marinade Dinki A Roba Meh Zurfi Idan Baki Da Buttermilk Seh Ki Hada Madara Da Vinegar Ko Lemun Tsami Chokali 2 Ki Barshi Tsawon M...
PreTime
more Minutes
CookTime
a few Minutes
Yield
Some Servings
Sent by mhhadejia
at : July 2, 2026
Step:
Da farko ki hada kayan marinade dinki a roba meh zurfi idan baki da buttermilk seh ki hada madara da vinegar ko lemun tsami chokali 2 ki barshi tsawon minti 10 ko 15 seh kiyi amfani da shi. Sai ki saka kazan cikin hadin ki rufe ki barshi yayi kaman awa 3 ko 4 ko ki barshi ya kwana cikin fridge.
Ki samu wani roba ki zuba kwai, gishiri,madara ki kada ya hade seh ki aje gefe.Cikin wani roban kuma ki sa flour,gishiri,ki marmasa cornflakes ki zuba ciki,masoro,oregano,mixed herbs ki juya sosai ki aje gefe.
Ki dakko kazar da kika sa cikin marinade ya tsumu seh ki tsame ki sa a tukunya ki sa albasa da tarugu da dandano seh ki dora kan wuta amma kar ki sa wuta da yawa kuma kar ki zuba ruwa.ki na yi kina dan girgiza tukunyar saboda kar ki juya ya fashe.idan ya dan kame jikinshi seh ki sauke kar ki barshi ya sha wuta kar ya fashe.ki tsane shi a colander ya huce.
Idan ya huce seh ki na daukan naman daya bayan daya kina sawa cikin hadin flour ki bade shi ko ina yaji hadin seh ki aje a plate har ki gama.
Idan kin gama seh ki sake dauka daya bayan daya wanda kika sa cikin hadin flour ki tsoma cikin hadin kwai ki sake sawa a cikin hadin flour seh ki aje a plate
Idan kin gama gaba daya seh ki dora mai a wuta idan yayi zafi seh ki soya.