KFC Chicken

Source : Da Farko Ki Hada Kayan Marinade Dinki A Roba Meh Zurfi Idan Baki Da Buttermilk Seh Ki Hada Madara Da Vinegar Ko Lemun Tsami Chokali 2 Ki Barshi Tsawon M...

PreTime
more Minutes
CookTime
a few Minutes
Yield
Some Servings

Sent by

at : July 2, 2026

Step:

  1. Da farko ki hada kayan marinade dinki a roba meh zurfi idan baki da buttermilk seh ki hada madara da vinegar ko lemun tsami chokali 2 ki barshi tsawon minti 10 ko 15 seh kiyi amfani da shi. Sai ki saka kazan cikin hadin ki rufe ki barshi yayi kaman awa 3 ko 4 ko ki barshi ya kwana cikin fridge.

    KFC Chicken recipe step 1 photo
  2. Ki samu wani roba ki zuba kwai, gishiri,madara ki kada ya hade seh ki aje gefe.Cikin wani roban kuma ki sa flour,gishiri,ki marmasa cornflakes ki zuba ciki,masoro,oregano,mixed herbs ki juya sosai ki aje gefe.

  3. Ki dakko kazar da kika sa cikin marinade ya tsumu seh ki tsame ki sa a tukunya ki sa albasa da tarugu da dandano seh ki dora kan wuta amma kar ki sa wuta da yawa kuma kar ki zuba ruwa.ki na yi kina dan girgiza tukunyar saboda kar ki juya ya fashe.idan ya dan kame jikinshi seh ki sauke kar ki barshi ya sha wuta kar ya fashe.ki tsane shi a colander ya huce.

    KFC Chicken recipe step 3 photo
  4. Idan ya huce seh ki na daukan naman daya bayan daya kina sawa cikin hadin flour ki bade shi ko ina yaji hadin seh ki aje a plate har ki gama.

    KFC Chicken recipe step 4 photo KFC Chicken recipe step 4 photo
  5. Idan kin gama seh ki sake dauka daya bayan daya wanda kika sa cikin hadin flour ki tsoma cikin hadin kwai ki sake sawa a cikin hadin flour seh ki aje a plate

    KFC Chicken recipe step 5 photo KFC Chicken recipe step 5 photo
  6. Idan kin gama gaba daya seh ki dora mai a wuta idan yayi zafi seh ki soya.

    KFC Chicken recipe step 6 photo

Ingredients

  1. 4 parts Kazan agric
  2. Marinade:
  3. Gishiri daidai bukata
  4. 1 Ginger garlic paste chokali babba
  5. 2 Buttermilk kofi
  6. Coating:
  7. 1 Flour kofi
  8. 1 Kwai
  9. Cornflakes 1/4 kofi
  10. Oregano 1/2 karamin chokali
  11. Madara1/4 kofi
  12. Gishiri yadda ake bukata
  13. Masoro 1/2 karamin chokali(dakakke)
  14. Mixed herbs1/2 karamin chokali
  15. Tarugu yadda ake bukata
  16. Albasa madaidaiciya
  17. Mai na suya

Related Recipes

Dafadukar shinkafa da busashen kifi

Dafadukar shinkafa da busashen kifi

Chocolate sauce/frosting

Chocolate sauce/frosting

Grilled chicken

Grilled chicken

Parpesun naman rago

Parpesun naman rago

Pizza sauce

Pizza sauce

DIY Carrot Oil

DIY Carrot Oil

Miyar gyada

Miyar gyada

Yoghurt

Yoghurt