Sandwich a saukake

Source : Ga Kayayyakin Da Za Ayi Amfani Da Su Nan A Wanke Nikakken Nama A Tsane A Kwalanda Sannan A Dora Shi Akan Wuta Saka Maggi Kori Kayan Kamshi Da Albasa ...

PreTime
more Minutes
CookTime
a few Minutes
Yield
Some Servings

Sent by

at : May 15, 2026

Step:

  1. Ga kayayyakin da za ayi amfani da su nan.

    Sandwich a saukakematakin girki1 hoto
  2. A wanke nikakken nama a tsane a kwalanda sannan a Dora shi akan wuta. Saka maggi, kori, kayan kamshi da albasa a zuba ruwa barshi ya dahu har ruwan ya kafe a jikinsa sai a sauke

    Sandwich a saukakematakin girki2 hoto
  3. A wanke Kara's a kankare bayan sai a yanyankashi a kwance, sannan a wanke tumatir da cucumber a yayyanka su a kwance. A yayyanka dafaffen kwai ma a kwance.

    Sandwich a saukakematakin girki3 hoto
  4. A Dora kasko akan wuta a zuba mai kadan sannan a saka yankakkiyar albasa da Dan yawa a juya, Idan ya fara soyuwa sai a saka attaruhu da albasa a juya na minti 5 sai a zuba Kara's shima na minti 5 a juya sai a kawo nikakken nama da aka dafa a zuba a kara spices sai a barshi mintuna 2 a sauke.

  5. A dauko fallen bread a zuba hadin naman akai

    Sandwich a saukakematakin girki5 hoto
  6. Sannan a saka tumatir, cucunber da kwai.

    Sandwich a saukakematakin girki6 hoto
  7. Daganan sai a kara zuba hadin naman akai a rufe da daya fallan bread din.

    Sandwich a saukakematakin girki7 hoto
  8. Sannan sai ake sakawa a manual toaster a gasa. Idan gefe yayi sai a juya gefe ma.

    Sandwich a saukakematakin girki8 hoto
  9. Idan ya gasu sai a cire. Acishi da duminsa yafi dadi

    Sandwich a saukakematakin girki9 hoto

Ingredients

  1. Bread me yanka yanka
  2. 5 Karas manya guda
  3. 2 Cucumber manya guda
  4. 5 Tumatir masu kyau guda
  5. 1 Albasa Babba guda
  6. 7 Dafaffen kwai guda
  7. Nikakken nama Rabin kilo
  8. Magi domin dandano
  9. Jajjagen tarugu da albasa cokali 1
  10. Curry
  11. Spices
  12. Mai cokali 2

Related Recipes

French toast + yam ball

French toast + yam ball

Wainar gero ta musamman

Wainar gero ta musamman

Shawarma

Shawarma

Potatoes patties

Potatoes patties

Makaroni da mai da yaji

Makaroni da mai da yaji

Spice Paratha

Spice Paratha

Kwalama bread me hadi

Kwalama bread me hadi

Lemon yalo da danyar citta

Lemon yalo da danyar citta