Source : A Gyara Wake A Cire Duwatsun A Wanke Sai A Markadaayi Amfani Da Abin Tata Mai Kyau A Tace Shi Sai A Zuba Ruwan A Tukunya A Dora A Wuta Idan Ya Kusa Ta...
PreTime
more Minutes
CookTime
a few Minutes
Yield
Some Servings
Sent by ummusabeer
at : December 26, 2025
Step:
A gyara wake a cire duwatsun a wanke sai a markada
Ayi amfani da abin tata mai kyau a tace shi, sai a zuba ruwan a tukunya a dora a wuta, idan ya kusa tafasa sai a jika dan tsami da ruwa kadan a juye ruwan a cikin tukunyan ruwan awaran su tafasa tare, zaa ga ta hade gu daya ruwan kuma ya koma kasa
Sai ayi amfani da abun Tara mai kyau a juye a ciki sai a daure har sai ruwan ya tsane sannan a kunce a yayyanka yadda ake so
Sai a jika farin maggi a ruwa ana tsoma awaran a ciki sannan a cire a saka cikin kwano
Sai a dora mai a wuta, idan yayi zafi, zaa fasa kwai a kwano a kada shi sai a tsoma awaran sannan a sa a mai a soya