Source : Da Farko Zaki Samu Alkama Ki Cire Datti Da Duwatsu Ki Kai Inji A Barza Ki Raba Tsaqin Da Garin Sai Ki Debi Kama Garin Gwangwani Daya Ki Hada Da Barjajj...
PreTime
more Minutes
CookTime
a few Minutes
Yield
Some Servings
Sent by Fatima Ibrahim(Albint,s Cuisine)
at : December 25, 2025
Step:
Da farko zaki samu alkama ki cire datti da duwatsu ki kai inji a barza ki raba tsaqin da garin sai. ki debi Kama garin gwangwani daya ki hada da barjajjen ki zuba mai rabin gwangwani ki hada shi sai ki xuba ruwan tsamiya ki hada shi sai ki ajiye shi kaman na hour uku
After 3 hours sai ki zuba a turmi ki kirba shi ya da ku sosai,kina Dan zuba ruwa kina daka wa
Gashi nan ya daku
Ga shi nan ya hadu
Ki shafa butter a hannun ki sai ki miqar da shi
Ki yi twisting,
Ki lankwasa shi kaman haka
Ki jera su akan tray
Ki soya shi a cikin mai, mai zafi
Ki zuba ruwa a tukunya sai kisaka sugar ki yanka lemon tsami ki zuba ki bar shi yayi kaman hour daya yana tafasa