Source : Wanke Kayan Miyanki Gabadata Ki Markada Ki Ajiye A Gefesami Shinkafa Mai Kyau Ki Bayar A Barzamiki Idan An Kawo Sai Ki Rairaye Ki Fitar Da Garin Sai Ki...
PreTime
more Minutes
CookTime
a few Minutes
Yield
Some Servings
Sent by ummusabeer
at : November 11, 2025
Step:
Wanke kayan miyanki gabadata ki markada ki ajiye a gefe
Sami shinkafa mai kyau ki bayar a barzamiki idan an kawo sai ki rairaye ki fitar da garin, sai ki wanke tsakinki tas da ruwa mai kyau
Ki dora tukunya a wuta tare da mai isasshe idan yayi zafi sai ki zuba markadan ki kidan soya sama sama sannan ki kara ruwa ki rufe har sai ya tafasa
Zaki zuba su Maggi, salt, curry, thyme, da garlic powder sannan ki kawo wankakken tsakinki ki zuba a cikin tukunyar ki gauraya
Sai ki rage wuta kina dubawa idan ya kusa dahuwa sai ki zuba alayyahunki wanda tuni kin gyara shi kin aje a gefe,sai ki barshi ya karasa sannan ki sauke