Zaa dauko attaruhu a wanke a jajjaga, a wanke albasa da tattasai a yankasu yadda akeso sai a zuba mai a kasco kadan idan yayi zafi sai a zuba albasar a juya daga nan sai a zuba attaruhu da tattasai a juya, a zuba magi thyme, curry a juya sai a kawo marmashen kifin a zuba a yi ta juyawa har sai yayi sai a sauke.