Source : Zaki Barza Shinkafa Saiki Wanke Tsakin Ki Aje Ki Gyara Zogala Ki Wanke Itama Ki Jajjaga Tattasai Da Tarugu Zaki Hada Shinkafar Da Zogala Kiyi Mixing ...
PreTime
more Minutes
CookTime
a few Minutes
Yield
Some Servings
Sent by Umman Amir And Minaal
at : June 7, 2026
Step:
Zaki barza shinkafa, saiki wanke tsakin ki aje, ki gyara zogala ki wanke itama, ki jajjaga tattasai da tarugu.
Zaki hada shinkafar da zogala kiyi mixing sosai, saikisa ruwa a pot, ki Dora a wuta ki dora kwando (kwalanda) a Kai, saiki nemi buhu ki yanka, ki wankeshi, saiki shinfidashi a cikin kwandon
Ki kawo hadin tsakin shinkafa da zogala ki zuba, saiki barshi ya turara kamar minti 15 saiki sauke ki juye a roba mai dan girma
Saiki sa tarugu, tattasai, albasa, mangyada, curry, kayan kamshi kiyi mixing sosai komai ya hade, saiki kara mayar dashi a cikin kwandon ya kara turara kamarna minti 10 saiki sauke shikenan... Aci da zafi..