Fura

Source : Da Farko Ki Surfa Geron Ki Bakace Dusar Seh Ki Wanke Ki Rege Tsakuwar Sai Ki Tsameshi A Colander Ya Tsane Bayan Ya Tsane Seh Ki Baza Shi A Tabarma Meh T...

PreTime
more Minutes
CookTime
a few Minutes
Yield
Some Servings

Sent by

at : May 13, 2026

Step:

  1. Da farko ki surfa geron ki bakace dusar seh ki wanke ki rege tsakuwar sai ki tsameshi a colander ya tsane.Bayan ya tsane seh ki baza shi a tabarma meh tsafta ya bushe.Idan ya bushe seh ki zuba kayan kanshi ki hada a niko miki.Idan an niko seh ki tankade da rariya meh laushi.

    Fura recipe step 1 photo Fura recipe step 1 photo Fura recipe step 1 photo
  2. Seh ki samu mazubi meh fadi ki juye garin amma ki rage kadan.Seh ki rika yayyafawa garin ruwa kadan kadan ki cakuda da hannu zaki ga Yana dunkulewa amma da sauran gari kina gani,seh ki cigaba da cakudawa yadda zaki dunkula shi ba tare da ya fashe ba.Seh ki dunkula shi da dan girma ki aje gefe,seh ki samu tukunya ki zuba ruwa kadan ki dora a wuta ya tafasa.

    Fura recipe step 2 photo Fura recipe step 2 photo Fura recipe step 2 photo
  3. Bayan ruwan ya tafasa seh ki sassaka curin garin da kika dunkula a ciki idan kinga ruwan yayi yawa ya wuce qwatan curin seh ki rage kadan ba a so ruwa yayi yawa ya sha kan curin seh ki rufe ki barshi ya dahu.Idan ya dahu zaki ga bayansa yayi ja kuma ruwan yayi kauri seh ki sauke ki dakko turmi ki saka curin daya bayan daya kina dakawa Yana fashewa har ki fasa duka curin idan kinason sikari yanzu Zaki saka seki cigaba da dakawa.Seh ki dibi ruwan dahuwar kadan ki zuba a ciki ki ci gaba da kirbawa

    Fura recipe step 3 photo Fura recipe step 3 photo Fura recipe step 3 photo
  4. Idan ya daku ya hade jikinsa Seh ki kwashe ki cura shi iyya girman da kike so,Seh ki dakko garin da Kika rage ki saka su a ciki ko Ina ya ji.

    Fura recipe step 4 photo Fura recipe step 4 photo Fura recipe step 4 photo
  5. Seh ki barshi ya Sha iska.A Sha fura lafiya.

    Fura recipe step 5 photo

Ingredients

  1. Gero Kofi -4
  2. Chitta busashe guda biyar
  3. Kanumfari babban chokali -1
  4. Masoro babban chokali -1
  5. Barkono guda -4
  6. Sikari dai dai bukata(optional)
  7. Ruwa dai dai bukata

Related Recipes

Soyayyen kwai meh vegetables da bredi gashin frying pan

Soyayyen kwai meh vegetables da bredi gashin frying pan

Buttermilk waffles

Buttermilk waffles

Kunun gyada meh cucumber

Kunun gyada meh cucumber

Spicy sausage samosa rolls

Spicy sausage samosa rolls

Soft and fluffy puff puff

Soft and fluffy puff puff

Stuffed potato balls

Stuffed potato balls

Mandula

Mandula

Tuwon plantain

Tuwon plantain