Idan ya hade amma da sauran flawa kadan seh ki juye hadin a kan work surface dinki da sauran flawar seh ki cigaba da murzawa da hannun ki har seh ya hade.idan ya hade seh ki cigaba da murzawa kina kneading har seh ta murzu ta hada jikinta,seh ki sa wuka ki tsaga tsakiyar flawar idan kinga cikin ta yayi sumul ba ramuka toh tayi amma idan da ramuka ki cigaba da murzawa har seh tayi sumul.