Dafadukar spaghetti da macaroni

Source : Da Farko Ki Dora Tukunya Akan Wuta Sai Ki Yanka Albasa Ki Zuba Mai Cikin Tukunyar Sai Ki Zuba Albasa Kadan Idan Ta Fara Soyuwa Sai Ki Zuba Ginger Garlic...

PreTime
more Minutes
CookTime
a few Minutes
Yield
Some Servings

Sent by

at : October 13, 2025

Step:

  1. Da farko ki dora tukunya akan wuta sai ki yanka albasa ki zuba mai cikin tukunyar sai ki zuba albasa kadan idan ta fara soyuwa sai ki zuba ginger garlic paste ki dan soya kadan sai ki zuba onion and pepper paste,idan ya dan soyu sai ki zuba jajjagen tumatir ki barshi ya soyu.

  2. Idan ya soyu sai ki zuba kayan kanshi da dandano ki sa gishiri kadan sai ki zuba ruwan nama ki zuba ruwa dai dai misali ki barshi ya tafaso sai ki zuba spaghetti bayan kin karya shi dai dai tsawon macaroni,sai ki zuba macaroni ki rufe.idan ya kusa nuna sai ki kawo kifinki soyayye bayan kin cire kayar kin fasa shi dai dai misali sai ki zuba ciki ki kara dandano ko kayan kanshi idan da bukata ki zuba sauran albasar idan da bukatar ki kara ruwa sai ki kara(yafi dadi da dan ruwa ruwa).

  3. Saj ki rufe ya karasa aci lafiya.


Ingredients

  1. Spaghetti rabin leda
  2. Macaroni rabin leda
  3. Onion and pepper paste leda daya
  4. Tumatir4 tattasai 2(a jajjaga)
  5. Albasa
  6. Soyayyen kifi (sardine)
  7. Dandano
  8. Kayan kanshi
  9. Mai
  10. Ruwa
  11. Ruwan tafashen nama
  12. Ginger garlic paste
  13. Gishiri

Related Recipes

Garlic Naan Bread

Garlic Naan Bread

Lemon Bundt cake

Lemon Bundt cake

Baked beans curry

Baked beans curry

Spicy crackers

Spicy crackers

Kunun zaki

Kunun zaki

Kunun aya meh kwakwa da dabino

Kunun aya meh kwakwa da dabino

Zebra cake

Zebra cake

Lemun malmo

Lemun malmo