Zaa wanke kayanmiya a markadasu sai a zuba mai cikin tukunya a dora a wuta abarshi ya yi zafi sai a zuba markadan a gauraya sannan a zuba maggi curry gishiri,dafaffan ganda tafarnuwa a sake gaurayawa sai a rufe a barshi ya dahu sannan a zuba garin agishin a gauraya sai a dauko yankakken kuma wakakken alayyahu a zuba agauraya sannan a sauke daga kan wuta. Zaa iya cin wannan miya tare da tuwon shinkafa semovita teba waina sinasir.