Kunun gyada meh cucumber

Source : Da Farko Zaki Gyara Gyadarki Sai Ki Tsince Dattin Sai Ki Zuba Mata Ruwan Zafi Tayi Kamar Minti 10 A Jike Sai Ki Tace Ki Surfa Ta Sama Sama A Turmi Kamar...

PreTime
more Minutes
CookTime
a few Minutes
Yield
Some Servings

Sent by

at : May 26, 2026

Step:

  1. Da farko zaki gyara gyadarki sai ki tsince dattin.sai ki zuba mata ruwan zafi tayi kamar minti 10 a jike sai ki tace ki surfa ta sama sama a turmi kamar yadda zaki surfa wake sai ki wanke tas bayan ya fita sai ki zuba mata ruwa ta dan kara jikuwa.idan ta jiku sai ki markada ki tace ki aje a gefe.

    Kunun gyada meh cucumbermatakin girki1 hoto
  2. Sai ki wanke cucumber dinki ki ki yanka ki zuba a blender ki nika sak ki tace.ki tanadi kullun shinkafar ki ki ajesu a gefe.

    Kunun gyada meh cucumbermatakin girki2 hoto
  3. Sai ki dora ruwan gyadarki a wuta ya tafaso.ki barshi ya dan tafasa saboda gafin gyadar ya wuce, amma asa ido kar ya tafaso ya zube.sai ki samu roba da zaki dama kunun ciki sai ki dibi kullunki dai dai yadda kikeso sai ki dama shi da wannan ruwan cucumber da kika tace.idan ruwan gyadar ya tafasa gafin ya fita sai ki sheka kan kullun ki juya.

  4. Sai kj zuba sugar da ruwan lemun tsami ki juya idan yayi kauri kina iya kara ruwan cucumber din ko ruwa dai dai yadda kikeso.

    Kunun gyada meh cucumbermatakin girki4 hoto

Ingredients

  1. Danyar gyada yadda kike bukata
  2. Kullun kamun shinkafa (da yaji kayan kamshi)
  3. Lemun tsami
  4. Cucumber
  5. Sugar
  6. Ruwa

Related Recipes

Dahuwar indomie a saukake

Dahuwar indomie a saukake

Alawar madara ta condensed milk

Alawar madara ta condensed milk

Couscous meh karas

Couscous meh karas

Potato pancakes

Potato pancakes

Fura

Fura

Dafadukar spaghetti da macaroni

Dafadukar spaghetti da macaroni

Lemun malmo

Lemun malmo

Nadaddentwistedbredi meh nutella

Nadaddentwistedbredi meh nutella