Shinkafa mai kayan lambu da miyar kayan ciki da dankali
Source : Ki Wanke Shinkafanki Saiki Tafasa Ta Ki Kara Wanketa Saiki Maidata Wuta Kisa Gishiri Da Dan Ruwa Kadan Ki Kara Turara Ta Saiki Sauke Ki Barta Tasha Isk...
PreTime
more Minutes
CookTime
a few Minutes
Yield
Some Servings
Sent by Zeesag Kitchen
at : March 23, 2026
Step:
Ki wanke shinkafanki saiki tafasa ta ki kara wanketa saiki maidata wuta kisa gishiri da dan ruwa kadan ki kara turara ta, saiki sauke ki barta tasha iska sosai.
Ki wanke kayan lambu saiki yanka yanda kikeso.
Kisa mai yay zafi saiki zuba cotta da tafarnuwa, karas, koren wake, albasa rabi, fis, kayan dandano da ataruhu ki juya saiki zuba shinkafan da albasa rabin da koren tattasai ki juya a hankali saiki bar ta turara.
Idan tayi saiki sauke kasa ki kawo foil paper ki daura akan shinkafan saiki zuba garwashi kadan Ki barbada mai cokali daya akan garwsshin zakiga ya fara hayaki saikiyi saauri ki rufe saboda anason hayakin ya shiga cikin shinkafan kamar minti biyar.
Ki fere dankalin ki saiki tafasashi a guda gudanshi.
Ki wanke kayan ciki saiki barshi ya tafaso saiki wanke shi tas sannan Kisa mashi kayan dandano da Albasa, kayan kamshi da ruwa ki barshi ya fara dahuwa saiki zuba jajjagaggen kayan miyanki da dankalin ki barsu su nuna.
Ingredients
4 Shinkafa Kofi
Kara's
Koren wake
Koren tattasai
Koren fis
Albasa
Ataruhu
Kayan dandano
Kayan kamshi
Dankalin turawa
Kayan cikin shanu
Tattasai
Tafarnuwa
Citta
Related Recipes
Gulab Jamun
Egg sauce
One pot potato casserole
Sofies Masala Dal Soup with cheese and sour cream
Vegetables cous cous with chicken and cabbage soup