Source : Nan Ga Abubuwan Da Muke Bukatada Farko Zaki Wanke Kayan Ciki Ki Sa A Tukunya Ki Hada Na Namanki Ki Zuba Maggi Sa Spices Masu Dadi Ki Tafasa Har Tsawon M...
PreTime
more Minutes
CookTime
a few Minutes
Yield
Some Servings
Sent by zhalphart kitchen
at : June 29, 2026
Step:
Nan ga abubuwan da muke bukata
Da farko zaki wanke kayan ciki ki sa a tukunya ki hada na namanki ki zuba maggi sa spices masu dadi ki tafasa har tsawon minti ashirin
Sai samu wata tukunyar ki zuba ruwan naman da ruwa kadan dai dai yawan miyarki saiki zuba nama da ganda da Kayan ciki da stock fish ki dafa minti sha biyar
Bayan ya dahu saiki zuba jajjgen attaruhu da albasa kisa daddawa ki juya sosai
Kisa maggi da gishiri ki juya saiki samu roba karami ki hada manja da ogbono ki juya
Saiki zuba aciki ki juya ki rage wutar ki barshi ya dahu minti ashirin amma ki dinga yi kina juyawa karya kone zakiga yayi yauki sosai.saiki zuba smoke fish dinki
Ki juya saiki kawo ganyenki ki zuba ki juya ki rufe bayan minti goma saiki sauke