Alkubus na alkama

Source : Da Farko Zaki Samu Garin Alkama Ki Zuba A Roba Meh Zurfi Seh Ki Zuba Yeast Mai Babban Chokali 2 Da Gishiri A Kai Ki Juya Seh Ki Rika Zuba Ruwan Dumi Ka...

PreTime
more Minutes
CookTime
a few Minutes
Yield
Some Servings

Sent by

at : March 17, 2026

Step:

  1. Da farko zaki samu garin alkama ki zuba a roba meh zurfi seh ki zuba yeast,mai babban chokali 2 da gishiri a kai ki juya.

    Alkubus na alkamamatakin girki1 hoto Alkubus na alkamamatakin girki1 hoto
  2. Seh ki rika zuba ruwan dumi kadan kadan ki kwaba da muciya ko hannu bayan kin wanke har seh ya hade amma kada yayi ruwa tsululu kuma kada yayi tauri,ki buga shi sosai seh ki sami kling film ki rufe ki sa waje meh dumi ya tashi.

    Alkubus na alkamamatakin girki2 hoto Alkubus na alkamamatakin girki2 hoto
  3. Bayan ya tashi seh ki sake buga shi,seh ki shafa mai a cikin mazubin da zaki zuba ki dibi kullun ki zuzzuba a ciki amma kar ki cika saboda zeh kara tashi seh ki jera cikin steamer ki rufe da buhu kar tiririn ya rika fita,ki zuba ruwan dumi cikin kasan steamer din ki dora kan wuta,idan ruwan na kara zafi zeh sa ya kara tashi kafin ya fara turaruwa.

    Alkubus na alkamamatakin girki3 hoto Alkubus na alkamamatakin girki3 hoto Alkubus na alkamamatakin girki3 hoto
  4. Idan ya turaru zaki ji kamshi ya cika Koina ko ki sa wuka ciki idan ta fito ba kullin a jiki alkubus dinki ya turaru.seh ki sauke, a ci da miyar taushe meh kabewa ko farfesu.

    Alkubus na alkamamatakin girki4 hoto Alkubus na alkamamatakin girki4 hoto

Ingredients

  1. Kofi 2 na garin alkama
  2. Yeast babban chokali 1
  3. Gishiri karamin chokali 1
  4. Ruwan dumi yadda ake bukata
  5. Mai

Related Recipes

Spicy crackers

Spicy crackers

Shepherds pie

Shepherds pie

Dafadukar macaroni

Dafadukar macaroni

Pani puri

Pani puri

One pot pasta

One pot pasta

Dafadukar penne pasta

Dafadukar penne pasta

Fried rice meh hanta

Fried rice meh hanta

Indomie pizza

Indomie pizza