Kunun Alkama

Source : Da Farko Zaki Samu Tukunya Ki Juye Ruwan A Ciki Seh Ki Zuba Madara Ki Juya Kina Iya Amfani Da Madarar Ruwa Ta Kwali Sannan Ki Zuba Garin Alkamar A Ci...

PreTime
more Minutes
CookTime
a few Minutes
Yield
Some Servings

Sent by

at : March 10, 2026

Step:

  1. Da farko zaki Samu tukunya ki juye ruwan a ciki seh ki zuba madara ki juya(kina iya amfani da madarar ruwa ta kwali).

    Kunun Alkama recipe step 1 photo Kunun Alkama recipe step 1 photo Kunun Alkama recipe step 1 photo
  2. Sannan ki zuba garin alkamar a ciki ki juya sosai da whisk ya zama ba gudaji.seh ki dora akan wuta kina juyawa akai akai idan ya dan fara kauri seh ki zuba garin habbahan ki cigaba da juyawa har seh yayi kauri amma a kula kada ya tafaso ya zube.

    Kunun Alkama recipe step 2 photo Kunun Alkama recipe step 2 photo
  3. Idan yayi kauri seh ki sauke ki zuba sikari ko zuma seh ki babbala dabinonki ki zuba akai da gyada.kina iya saka duk abin da kike so ko gyadar almond, kashew ko kayan marmari kamar ayaba ko busashen inabi.

    Kunun Alkama recipe step 3 photo Kunun Alkama recipe step 3 photo Kunun Alkama recipe step 3 photo

Ingredients

  1. Garin alkama rabin kofi(kar yayi laushi sosai)
  2. Kofi 4 na ruwa
  3. Madarar gari rabin kofi
  4. Sikari daidai bukata
  5. Rabin karamin chokali na Garin Habbahan(cardamom)
  6. Dabino (dai dai bukata)
  7. Gyada soyayya (dai dai bukata)

Related Recipes

Faten doya

Faten doya

Braised indomie tofu

Braised indomie tofu

Shelpek flat bread

Shelpek flat bread

Kalallaba

Kalallaba

Healthy sugar free Granola

Healthy sugar free Granola

Shepherds pie

Shepherds pie

DIY Carrot Oil

DIY Carrot Oil

Tuwon plantain

Tuwon plantain