Source : Ki Aza Ruwa Saman Wuta A Cikin Tukunya Sai Ki Jefa Kanwa Kadan A Ciki Ki Ruhe Idan Ya Tafasa Said Kisa Butter Kamar Babban Cokali Day Ki Samu Wuri Dab...
PreTime
more Minutes
CookTime
a few Minutes
Yield
Some Servings
Sent by Walies Kitchen N Small Chops
at : February 3, 2026
Step:
Ki aza ruwa saman wuta a cikin tukunya sai ki jefa kanwa kadan a ciki ki ruhe, idan ya tafasa said kisa butter Kamar babban cokali day, ki samu wuri daban ki dibi garin masara ki kwaba da ruwa kar yayi kauri sosai Kuma kar yayi ruwa sosai. Sai ki dauko hadin garin ki zuba acikin ruwan masu tafasa kina juyawa da muciya kar yayi gudaji Amma Zaki rage wutar idan yayi kauri sai ki rufe ki bashi lokaci ya dahu.
Idan ya dahu, sai ki raba biyu, ki zuba Rabin a want wuri ki ruhe ki bar Rabin a tukunya ki tuqa kina zuba gari kadan kadan kina tuqawa har kaurinshi yayi Miki sai ki yayyafa ruwa a sama ki ruhe ya qara dahuwa, idan ya dahu sai ki dauko wancan Rabin talgen da Kika aje ki zuba acikin ki tuqa sosai sai ya hade ki qara mintoci kadan ki sauke Amma kar ki Bari yayi qarhi ki Yishi da laushi, sai ki kwashe aci da miyar da akeso Amma yahi Dadi da miyar yauqi.