Source : Ki Wanke Gero Ki Jiqa Ya Kwana Idan Gari Ya Waye Ki Wanke Kisa Citta Dankali Yaji Kanumfari Da Kimba Sai Ki Kai A Markada Miki Idan An Markada Sai Ki...
PreTime
more Minutes
CookTime
a few Minutes
Yield
Some Servings
Sent by Walies Kitchen N Small Chops
at : January 22, 2026
Step:
Ki wanke gero ki jiqa ya kwana idan gari ya waye ki wanke kisa citta, dankali,yaji, kanumfari da kimba sai ki Kai a markada Miki. Idan an markada sai ki zuba ruwa ki tace da abin Tata, sai ki aje har ya kwanta.
Bayan ya kwanta ruwa ya taso sama sai ki tsiyaye ruwan ki taba gasarar 2; kashin farko ki tafasa ruwan zafi ki dama kunu, ki aje kunun sai ya huce Babu zahi ko kadan, dayan Kuma ki sa mishi ruwa ki motse sai ki hadesu tare da wancan hutaccen kunun kisa sugar kisa flavor ki motse sai kisa a na'ura Mai sanyaya Abu yayi sanyi sai a Sha.