Source : Da Farko Na Gyara Gyada Na Na Cire Yalla Da Kuma Mai Bori Na Ajiye A Gefe Na Fasa Kwai A Wani Kwano Na Zuba Sugar Flavor Da Dan Gishiri Na Kada Sosai...
PreTime
more Minutes
CookTime
a few Minutes
Yield
Some Servings
Sent by Fatima Ibrahim(Albint,s Cuisine)
at : December 1, 2025
Step:
Da farko na gyara gyada na na cire yalla da kuma mai bori, na ajiye a gefe, na fasa kwai a wani kwano na zuba sugar, flavor da dan gishiri na kada sosai ya hadu, a daya kwanon kuma na tankade fulawa
Anan na zuba kwai kadan na gauraya shi sai na Barbara fulawa na jujjuya shi, na sake zuba kwai na jujjuya
Na zuba fulawa na jujjuya, na zuba kwai
A haka za ayi tayi har sai gyadan ya rufe gaba daya idan an gama sai a juye a colander
Gashi ya gamu sai a daura mai a wuta a soya a soya a mai me zafi idan yayi ja sai a sauke a barshi yasha iska sai a ci