Source : Ki Jiqa Shinkafar Masa Tsawon Awa 3 Ko Da Dare Zuwa Safe Idan Ta Jiqa Sai A Wanke A Hada Da Dafaffiyar Shinkafa Asa Yeast Da Albasa Da Danyar Citta A M...
PreTime
more Minutes
CookTime
a few Minutes
Yield
Some Servings
Sent by Walies Kitchen N Small Chops
at : November 27, 2025
Step:
Ki jiqa shinkafar Masa tsawon awa 3 ko da dare zuwa safe, idan ta jiqa Sai a wanke a hada da dafaffiyar shinkafa asa yeast da albasa da danyar citta a markada.
Idan an markade yayi laushi sosai Sai aje wuri Mai dimi zuwa away 1 ko fiye, idan ya taso Sai asa baking powder da gishiri da sugar da kwai a motse ya hade. Sai a aza farantin Wanda bau kamawa a goga Mai kadan a zuba kullun a rufe wuta kadan, I Dan yayi hude hude shine ya gasu Sai a sauke asa wani har a Gama. Ba'a juyawa. Sai aci da kowace irin Miya akeso.