A wanke kayan miya sai a jajjagasu a zuba mai cikin tukunya a dora a wuta a zuba jajjagen a soyasu a zuba maggi garin tafarnuwa sai gauraya sannan a dauko daffiyar hanta a zuba,a rage wuta sai a zuba alayyahu a gauraya sai a rufe yayi minti 2 sai a sauke