Source : Ki Wanke Zobo Ki Zuba A Tukunya Saiki Zuba Citta Kanunfari Masoro Bawon Abarba Kimba Da Ruwa Ki Barsu Su Tafaso Zuwa Minti 10 Saiki Zuba Kanwa Sabod...
PreTime
more Minutes
CookTime
a few Minutes
Yield
Some Servings
Sent by Zeesag Kitchen
at : November 20, 2026
Step:
Ki wanke zobo ki zuba a tukunya saiki zuba citta, kanunfari, masoro, bawon abarba, kimba da ruwa ki barsu su tafaso zuwa minti 10 saiki zuba kanwa saboda tsami.
Ki wanke cucumber saiki yanka kanana kiyi blending dinta saiki zuba cikin zobon ki juya saiki barshi yasha iska sannan ki tace.
Kisa sugar, flavours da foster Clark's.
Ki yanka abarba saikiyi blending dinta da ruwa ki tace juice dinta sannan ki daura a wuta ki zuba sugar ya tafaso sosai. Saiki saka a fridge yayi sanyi.
Ga sauran hotunan
Nan ga duk abinda muke bukata wurin hada wannan lemon.
Ki fasa kankara saiki zuba a cup, ki kawo pineapple syrup ki zuba saiki zuba zobon akan lemon (amma akan kankaran ake zuba zobon cikin nutsuwa) idan ba haka ba zai hade.