Bidmis

Source : Da Farko Ki Dora Tukunya Akan Wuta Sai Ki Zuba Sikari Da Ruwa Idan Ya Narke Sai Ki Zuba Tsamiya Ki Barshi Ya Tafaso Sikarin Ya Narke Zakiga Yana Danko A...

PreTime
more Minutes
CookTime
a few Minutes
Yield
Some Servings

Sent by

at : September 12, 2025

Step:

  1. Da farko ki dora tukunya akan wuta sai ki zuba sikari da ruwa idan ya narke sai ki zuba tsamiya ki barshi ya tafaso sikarin ya narke,zakiga yana danko amma wuta kadan zaki sa kar ya kone kina dan juyawa akai akai.

    Bidmismatakin girki1 hoto Bidmismatakin girki1 hoto Bidmismatakin girki1 hoto
  2. Idan ruwan sikarin yayi dan ja kuma yana danko sai ki kawo gyadar ki zuba a ciki kina tukawa,har sai ya hade jikinsa.Ki cigaba da tukawa har ya hade sosai yayi kauri.sai ki samu leda ki shafa mata mai sai ki juye akan ledar ki samu rolling pin ki shafa masa mai idan ya dan sha iska sai ki sa rolling pin din ki fadada shi.

    Bidmismatakin girki2 hoto Bidmismatakin girki2 hoto
  3. Bayan ki fadada shi sai ki samu wuka ki shafa mata mai sai ki yanka duk shape din da kike so ki samu leda ki nade ki daure bakin kamar sweet.

    Bidmismatakin girki3 hoto Bidmismatakin girki3 hoto

Ingredients

  1. Nikarkiyar gyada (irin ta kunu wadda aka soya)kofi 1da rabi
  2. Sikari kofi biyu
  3. Tsamiya sili uku
  4. Mai (da za a shafa akan leda)

Related Recipes

Dan wake

Dan wake

Stuffed potato balls

Stuffed potato balls

Bredin kabewa meh rose

Bredin kabewa meh rose

Parpesun kaza meh dankali

Parpesun kaza meh dankali

One pot pasta

One pot pasta

Garlic Naan Bread

Garlic Naan Bread

Zebra cake

Zebra cake

Lemun malmo

Lemun malmo