Source : Ga Kayan Da Akayi Amfani Da Suacikin Ruwan Dumi Saa Saka Yeast Sikari Madara Madara Da Gishiri Sai Kisa Kwan Ki Aciki Ki Kada Sosai Kisa A Filawar Ki ...
PreTime
more Minutes
CookTime
a few Minutes
Yield
Some Servings
Sent by Sumy's delicious
at : August 8, 2026
Step:
Ga kayan da akayi amfani da su
Acikin ruwan dumi saa saka yeast,sikari,madara,madara da gishiri
Sai kisa kwan ki aciki ki kada sosai kisa a filawar ki
Ki juya sosai kwabin ki yazama yana dan mama hannun ki
Sai kisa shi a inda zaki buga shi ki sa butter da vanilla ki yi ta bugashi na tsawon mintuna 15
Bayan kin gama bugashi indai ya bugu zaki iya jan kwabin naki ki gani indai ya jawu sosai to kwabinki ya bugu sai kisamu kwano kisa butter kisa shi aciki ki rufe ki sa shi awaje mai dumi na awa daya. Zakiga ya tashi
Sai ki Kara mulmulashi kisamu abun gashi kisa butter ki barbada masa filawa sai kisa kwabin aciki yakara tashi na wani awa 1 to anan zaki iya shafa masa kadaddan kwai ki gasa shi to amma ni nadan yi wani salo
Kamar haka, kuma nayi amfani da filawa
Dan yan kawar danakeyi shi zai hana burudin tashi sosai karya bata kwalliyar saiki shafa kadaddan kwai ki gasa