Soyayyen kwai meh vegetables da bredi gashin frying pan
Source : Ki Hada Turmeric Chokali Daya Da Masoro Karamin Chokali Da Chitta 1/2 Karamin Chokali Ki Sa Maggi Daya Da Gishiri Kadan Ki Hadesu Waje Daya Ki Samu Roba...
PreTime
more Minutes
CookTime
a few Minutes
Yield
Some Servings
Sent by mhhadejia
at : August 2, 2026
Step:
Ki hada turmeric chokali daya da masoro karamin chokali da chitta 1/2 karamin chokali ki sa maggi daya da gishiri kadan ki hadesu waje daya ki samu roba ki juye duk sanda zaki soya kwai seh ki barbada a kai.
Ki samu frying pan seh ki sa mai kadan ki fasa kwanki a ciki kar ki kada seh ki zuba tumatir,albasa koran tattasai(yankakke) a kai ki dan rage wutan kadan seh ki barbada hadin turmeric a kai.
Idan ya soyu seh ki juya daya gefen a hankali ki kara barbada hadin turmeric a kai ki barshi ya soyu seh ki sa a plate.
Seh ki dakko bredinki ki gasa a kan frying pan din duka gefe biyun.kina iya sha da tea ko ki ci haka.