Source : Wadan Nan Sune Kayan Yin Wanan Kyakyawan Brodiki Zuba Ruwan Dumi A Roba Koh Kwanoseki Zuba Yeastkizuba Sukariki Zuba Madaraseki Zuba Filavorkijuya Sosai...
Sent by Mato's Favorite Dishes
Wadan nan sune kayan yin wanan kyakyawan brodi
Ki zuba ruwan dumi a roba koh kwano
Seki zuba yeast
Kizuba sukari
Ki zuba madara
Seki zuba filavor
Kijuya sosai
Daga nan seki juye filawan ki kiyi ta juyawa
Idan ya juyu seki zuba bota
Kiyi kneeding sosai har se botan ya shige
Ki zuba mangyada ki juya sosai har seyayi laushi
Seki rufeshi kisa a rana ya tashi
Bayan ya tashi seki Zuba filawa a kan tiran murji kisaka kwabin filawan ki mirza
Seki yi rolling yayi filat
Seki saka wuqa ki yanka a tsaytsaye
Sekiyi rolling dinshi kamar cinnamon rolls
Ki shafa bota ko mai a gwangwani ki saka a ciki
Haka zaki cigaba har seya cika
Seki tura a cikin oven ki barshi ya gasu kamar minti shabiyar hakan nan seki cire bayan yayi ki shafa mai a saman seci
Kiga yanda yayi fari yayi laushi ga dadai
Da fatan kun qaru sosai kuma zaku gwada.Da haka nake cewa mujima lfy Allah bar mana cookpad