Source : Hadin Miyar Kaza Zaa Cire Hancin Kayan Miya A Bare Albasa A Yanka Kanana A Wanke Da Ruwa A Markada Su Sannan A Juye Markadan Cikin Tukunya A Dora A Wut...
PreTime
more Minutes
CookTime
a few Minutes
Yield
Some Servings
Sent by ummusabeer
at : June 8, 2026
Step:
Hadin miyar kaza: zaa cire hancin kayan miya,a bare albasa a yanka kanana a wanke da ruwa a markada su sannan a juye markadan cikin tukunya a dora a wuta abarshi ya dahu sosai har sai ruwan ya kone sannan a sauke a aje agefe.
A gyara naman kaza a wanke a zuba cikin tukunya sannan a zuba yankakken albasa garin tafarnuwa citta a cakuda sai a rufe a barshi ya tafasa sai a sannan a sauke a tsame naman daga cikin ruwan a.zaa dora mai a wuta idan yayi zafi sai a soya wannan naman har a gama. Zaa dora tukunya a wuta a zuba manja idan yayi zafi sai a zuba dafaffan kayan miya ciki a gauraya sannan a zuba maggi curry kadan sai a kawo soyayyan nama a juye ciki a gauraya sannan a rufe a barshi ya dan dahu sai a sauke.
A wanke shinkafa sai ajika ta jiku a wanke sannan a markada. Zaa juye markadan a cikin tukunya ko bokitin roba a zuba yeast suga a gauraya sannan a rufe a barshi wajan dumi ya tashi sannan a zuba baking powder kadan a gauraya sai a dora tanda kan wuta a zuba mai cokali daya ko biyu sannan a zuba kullin da ludayi a soya har sai yayi sannan a juya shima cikin ya soyu.
A bare kabewa a yanka yadda akeso sai a wanke ta a zuba a cikin tukunya a dafa ta dahu sannan a tsame a wanke kayan miya a hada a markada gaba daya.zaa juye markadan cikin tukunya a dora a wuta a zuba manja maggi ruwan naman kaza garin tafarnuwa a barshi ya tafasa sai a yankakken wankakken alayyahu a gauraya sai a sauke tururin zai karasa dafashi.