Source : Da Farko Dai Bayan Kin Wanke Waken Ki Sai Ki Dora Shi Akan Wuta Ki Dan Tarfa Kanwa Ki Barshi Ya Dahu Shi Saka Kanwa Zaisa Waken Ya Dahu D Awuri Sannan ...
PreTime
more Minutes
CookTime
a few Minutes
Yield
Some Servings
Sent by Ummee Irfan Kitchen
at : March 20, 2026
Step:
Da farko dai bayan kin wanke waken ki sai ki dora shi akan wuta ki dan tarfa kanwa ki barshi ya dahu shi saka kanwa zaisa waken. Ya dahu d awuri sannan zai baki kalar ainiihin garau garau
Bayan kin waken ki ya dahu sai ki sauke ki tace sai ki kara ruwa ki dora shinkafarki ki barta ta kusa tsotsewa sai ki zuba maggi da dan gishiri ki barshi ya tsotse ruwan tas
Sai ki dauko dan cabbage idan kinaso d salat da tumatir ki yanka siri siri sai ki wanke da gishiri
Sai ki samu manja ko magyada sai ki soya shi da dan albasa sama sama zakiji yana kamshi sai ki sauke sai ki shirya abincinki akan plate wannan
Nb wasu basu son kanwa sai su saka albasa wurin dahuwar waken amma ni ina saka kanwa saboda kalar shinkafar ta dan canza