Shinkafa da wake aka garau garau

Source : Da Farko Dai Bayan Kin Wanke Waken Ki Sai Ki Dora Shi Akan Wuta Ki Dan Tarfa Kanwa Ki Barshi Ya Dahu Shi Saka Kanwa Zaisa Waken Ya Dahu D Awuri Sannan ...

PreTime
more Minutes
CookTime
a few Minutes
Yield
Some Servings

Sent by

at : March 20, 2026

Step:

  1. Da farko dai bayan kin wanke waken ki sai ki dora shi akan wuta ki dan tarfa kanwa ki barshi ya dahu shi saka kanwa zaisa waken. Ya dahu d awuri sannan zai baki kalar ainiihin garau garau

  2. Bayan kin waken ki ya dahu sai ki sauke ki tace sai ki kara ruwa ki dora shinkafarki ki barta ta kusa tsotsewa sai ki zuba maggi da dan gishiri ki barshi ya tsotse ruwan tas

  3. Sai ki dauko dan cabbage idan kinaso d salat da tumatir ki yanka siri siri sai ki wanke da gishiri

  4. Sai ki samu manja ko magyada sai ki soya shi da dan albasa sama sama zakiji yana kamshi sai ki sauke sai ki shirya abincinki akan plate wannan

  5. Nb wasu basu son kanwa sai su saka albasa wurin dahuwar waken amma ni ina saka kanwa saboda kalar shinkafar ta dan canza

    Shinkafa da wake aka garau garau recipe step 5 photo

Ingredients

  1. Shinkafa gwangwani daya
  2. Wake rabin gwangwani
  3. Kanwa
  4. Maggi star
  5. Haddadiyar yaji mai kayan kamshi
  6. Salat da tumatir
  7. Gishiri
  8. Cabbage

Related Recipes

Buffalo deviled eggs

Buffalo deviled eggs

Kwadon zogalemoringa

Kwadon zogalemoringa

Spicy dish of Tofu and minced meat

Spicy dish of Tofu and minced meat

Watermelon smoothie

Watermelon smoothie

Fenugreek leaves and potato masala

Fenugreek leaves and potato masala

Irish wif veggies

Irish wif veggies

Smoky Red Pepper Chili Chicken

Smoky Red Pepper Chili Chicken

Fries

Fries