Source : Da Farko Zaki Wanke Tsakin Ki Tas Ki Aje A Gefe Sai Ki Yanka Alaiyahunki Ki Wanke Shima Ki Aje A Gefe Sai Ki Dan Daka Gyadarki Shima Ki Aje A Gefeki D...
PreTime
more Minutes
CookTime
a few Minutes
Yield
Some Servings
Sent by Ayyah's Kitchen
at : July 15, 2026
Step:
Da farko zaki wanke tsakin ki tas ki aje a gefe, sai ki yanka alaiyahunki ki wanke shima ki aje a gefe, sai ki dan daka gyadarki shima ki aje a gefe
Ki dora tukunya a wuta sai kisa mangyada ki soya markaden kayan miyanki anya soyu dai ki zuba maggi, gishiri, kayan kamshi sai ki tsaida sanwa, sai ki dakko gyadar nan kisa su tafaso tare
Bayan ya tafasa sai ki zuba tsakinki kina juya kiyita juyawa har yayi kauri sabida kar ya kwanta a kasa. In yayi kauri sai ki barshi ya dahu. Daganan sai ki zuba dafaffen waken ki Kafin ya gama dahuwan sai ki zuba alaiyahunki ki barshi na mintuna biyar. Shikenan kin gama paten tsakin ki