Shredded beef sauce da couscous

Source : Da Farko Zaki Zuba Naman Ki A Roba Ki Zuba Kayan Hadin Da Na Lissafa Na Marinade Ki Juya Sosai Ko Ina Ya Samu Seh Ki Rufe Ki Sa A Fridge Ya Samu Kamar A...

PreTime
more Minutes
CookTime
a few Minutes
Yield
Some Servings

Sent by

at : June 12, 2026

Step:

  1. Da farko zaki zuba naman ki a roba ki zuba kayan hadin da na lissafa na marinade ki juya sosai ko ina ya samu seh ki rufe ki sa a fridge ya samu kamar awa daya.Daman kin riga kin yayyanka su carrot dinki duka kiyi musu yankan tsaye.

    Shredded beef sauce da couscousmatakin girki1 hoto Shredded beef sauce da couscousmatakin girki1 hoto Shredded beef sauce da couscousmatakin girki1 hoto
  2. Ki dora pan dinki a wuta seh ki zuba mai kadan ki zuba naman,idan ya dan kame seh ki zuba albasa,dandano da kayan kanshi ki dan zuba ruwa ki juya ki barshi ya dan sulala,sannan ki kawo vegetables dinki ki zuba ki juya ya dan Samu minti biyu.

    Shredded beef sauce da couscousmatakin girki2 hoto Shredded beef sauce da couscousmatakin girki2 hoto Shredded beef sauce da couscousmatakin girki2 hoto
  3. Seh ki dama corn flour da dan ruwa kadan ki zuba don yayi kauri,idan yayi Kamar minti biyu seh ki kara gishiri idan da bukata ki sauke.

    Shredded beef sauce da couscousmatakin girki3 hoto Shredded beef sauce da couscousmatakin girki3 hoto
  4. Seh ki dafa couscous dinki,ki samu tukunya ki zuba ruwan seh ki zuba Mai Kamar chokali biyu a cikin ruwan ki sa dan gishiri kadan da Maggi ki zuba turmeric seh ki barshi ya tafasa,idan ya tafasa seh ki zuba sweet corn dinki da peas(nayi amfani da na gwangwani)seh ki rika zuba couscous din kadan kadan kina juyawa ya hade da ruwan seh ki rufe da foil ki sa murfin tukunya ki rufe ki kashe wutar ki barshi yayi Kamar minti shabiyar seh ki sa fork ki barbazashi seh ki kwashe.

    Shredded beef sauce da couscousmatakin girki4 hoto Shredded beef sauce da couscousmatakin girki4 hoto Shredded beef sauce da couscousmatakin girki4 hoto
  5. Tip: idan zaki dafa couscous ana so ki sa ruwan daidai adadin couscous din zeh yi wara wara kuma ba zeh chabe ba.


Ingredients

  1. Hadin sauce:
  2. Shredded beef Kofi biyu
  3. Carrot yankake kofi daya
  4. Kore da Jan tattasai yankake duka Rabin kofi
  5. Albasa yankakkiya Kofi daya
  6. Tumatir yankake Rabin kofi
  7. Dandano da kayan kanshi
  8. Corn flour babban chokali biyu,ruwa dai dai bukata
  9. Kayan tsuma (marinade)nama:sesame oil da vinegar chokali dai dai
  10. Soy sauce,oyster sauce,barbecue sauce, karamin chokali dai dai
  11. Chilli sauce,Maggi na ruwa karamin chokali dai dai
  12. Tafarnuwa da chitta dai dai misali
  13. Kayan hadin couscous:
  14. Couscous Kofi biyu
  15. Ruwa Kofi biyu
  16. Gishiri kadan
  17. Turmeric 1/4 karamin chokali
  18. Mai babban chokali biyu
  19. Maggi knorr guda daya
  20. Sweet corn da peas Rabin kofi

Related Recipes

Spicy crackers

Spicy crackers

Flaky crispy samosa dough recipe

Flaky crispy samosa dough recipe

Moist and fudgy chocolate cake

Moist and fudgy chocolate cake

Pita bread pockets

Pita bread pockets

Carrot drink

Carrot drink

Faten doya

Faten doya

Shredded beef sauce da couscous

Shredded beef sauce da couscous

KFC Chicken

KFC Chicken