Tsala

Source : Da Farko Ki Wanke Geron Ki Rege Seh Ki Jika Shi Tsawon Awa 4 Ko 5 Idan Ya Jiku Seh Ki Kai Nika Ko Ki Nika A Blender Amma Kar A Cika Ruwa Bayan An Nika ...

PreTime
more Minutes
CookTime
a few Minutes
Yield
Some Servings

Sent by

at : February 22, 2026

Step:

  1. Da farko ki wanke geron ki rege seh ki jika shi tsawon awa 4 ko 5.Idan ya jiku seh ki kai nika ko ki nika a blender amma kar a cika ruwa.

    Tsalamatakin girki1 hoto Tsalamatakin girki1 hoto
  2. Bayan an nika seh ki zuba garin alkama ko flour amfanin hakan don ya sa Shi danko saboda gero ba shi da danko.sannan ki zuba yeast ki juya sosai seh ki rufe da kling film ki sa shi waje meh dumi ya tashi.

    Tsalamatakin girki2 hoto
  3. Bayan ya tashi seh ki zuba karkashi,gishiri,da sikari ki juya idan da tsami seh ki zuba ruwan kanwa ko baking powder kadan ki juya ya hade sosai.

    Tsalamatakin girki3 hoto Tsalamatakin girki3 hoto Tsalamatakin girki3 hoto
  4. Seh ki dora mai a wuta idan yayi zafi seh ki rika diba da karamin chokali ko ludayi kamar dai yadda ake suyan kosai kina zubawa a mai,idan yayi ja seh ki juya dayan gefen shima idan yayi ja seh ki kwashe ki tsane a colander.

    Tsalamatakin girki4 hoto Tsalamatakin girki4 hoto
  5. Dama kin riga kin hada yajin kulin ki,ki samu kuli ki sa barkono kadan da maggi da dan gishiri ki daka seh aci dashi amma ba a cika mishi barkono.Aci lafiya

    Tsalamatakin girki5 hoto

Ingredients

  1. Gero surfaffe
  2. Garin alkama ko flour rabin kofi
  3. Busashen karkashi chokali 1
  4. Yeast chokali 1
  5. Gishiri dai dai bukata
  6. Sikari dai dai bukata
  7. Ruwan kanwa ko baking powder kadan
  8. Mai na suya

Related Recipes

Faten acca

Faten acca

Indomie pizza

Indomie pizza

Chocolate Cupcakes

Chocolate Cupcakes

Left over stir fried rice

Left over stir fried rice

Yoghurt

Yoghurt

KFC Chicken

KFC Chicken

Home made golden syrup

Home made golden syrup

Dan wake

Dan wake