Ki tafasa nama da kayan kamshi saiki daka a turmi. Ki yanka albasa ki soyata sama sama saiki, ki zuba nama, maggi, ataruhu, koren tattasai, kori. Sannan ki soya sama sama. Ki murza fulawa saiki cire shape din da kikeso ki zuba nama, ki rufe da folk. Sannan ki soya a mai mai zafi